Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya kori ma’aikata 513 na sashin wasanni na jihar.
Matakin da Godwin Obaseki ya fara aiki, tun daga Litinin 21 ga watan Maris, 2022.
Sallamar ma’aikatan da Vanguard ta rawaito cewa, na cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ranar 4 ga watan Maris, 2022, kuma waɗan da lamarin ya shafa ya kunshi manya da ƙananan ma’aikata.
Matakin wani bangare ne na kokarin da take na sauya salon sashin wasanni zuwa hukumar wasanni ta jihar Edo.