Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya kara albashi mafi karanci a ma’aikatan jihar zuwa N70,000, daga ranar 1 ga Mayu, 2024.
Obaseki ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wurin kaddamar da gidan kwadago, wanda aka gina domin kungiyoyin kwadago a jihar.
An sanya wa gidan sunan tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomhole.
Obaseki ya ce gwamnatinsa za ta kara sabon mafi karancin albashin ma’aikatan jihar daga N40,000 zuwa N70,000.
Ya kuma yi alkawarin kara albashin ma’aikata sama da N70,000 duk wata idan gwamnatin tarayya ta amince da q sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan.
A cewarsa, za a sanar da al’umma cikakken bayani kan sabon mafi karancin albashin a yayin bikin ranar ma’aikata ta bana a ranar Laraba 1 ga watan Mayu.