Gwamnan jihar Edo a kudancin Najeriya ya ƙara yawan albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikata daga N70,000 zuwa N75,000.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya Nan ya ruwaito Gwamna Monday Okpebholo na bayyana hakan a birnin Benin yayin jawabinsa na jiya Alhamis a bikin Ranar Ma’ikata.
“A yau ina mai farin cikin sanar da cewa gwamnatinmu ta amince da sabon albashi mafi ƙanƙanta na N75,000 ga dukkan ma’aikatan Edo,” in ji shi.
“Wannan wata hanya ce ta gode muku ma’aikatan Edo. Mun yi imanin hakan zai yi tasiri ƙwarai kuma mun dogara da jajircewarku wajen inganta jihar Edo.”
Har yanzu akwai jihohin Najeriya da ba su fara biyan mafi ƙanƙantar albashi na N70,000 ba, wanda gwamnatin tarayya ta ayyana a watan Yulin 2024.