Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta, ya bada umarnin dakatar da kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar Omoun Perez cikin gaggawa.
A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Dr. Kingsley Emu, ya ce gwamnan ya kuma umarci babban sakataren ma’aikatar, Bennett Agamah; Mataimakin Darakta, Injiniyan Aikin Noma, Oki Yintareke; da Babban Akanta, Gabriel Idiatacheko, ya ci gaba da tafiya hutun dole har sai an samu sanarwa daidai da ka’idojin ma’aikatan gwamnati.
Ya bayyana cewa matakan sun zama wajibi ne biyo bayan nazarin aiwatar da aikin Greenhouse da ma’aikatar noma da albarkatun kasa ta jihar ta yi.
Sannan ta ce an dauki matakin ne sakamakon rahoton wucin gadi na kwamitin da kuma samun damar samun bayanai ba tare da wani cikas ba a lokacin gudanar da bincike.
“Oborevwori ya kafa wani kwamiti na mutum bakwai karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar, Dr. Kingsley Emu, don bincikar da’awar da kuma fahimtar rashin gaskiya da ke da alaka da gudanar da shirin ta ma’aikatar,” in ji shi.
Ya ce matakin da gwamnati ta dauka ba wai wani zato ne na laifi ba, sai dai matakin da ya dace don tabbatar da tsarkin tsarin binciken da aka riga aka kafa wanda shi ne tabbatar da cewa an gudanar da binciken ba tare da wani tasiri da bai dace ba ko kuma son zuciya.