fidelitybank

Gwamnan Bayelsa ya sake lashe zabensa

Date:

Gwamnan Bayelsa kuma ɗan takarar jam’iyyar PDP, Douye Diri, ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Mista Diri ya samu wa’adi na biyu ne bayan Baturen Zaɓe Farfesa Faruq Kuta ya bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’a 175,196.

Ɗan takarar adawa na APC, Timipre Sylva, shi ne ya zo na biyu da ƙuri’a 110,108, sai kuma Udengs Eradiri na jam’iyyar LP a mataki na uku da ƙuri’u 905.

Sakamakon ƙaramar hukuma biyu na Kudancin Ijaw da Brass ne suka jawo ɗage tattara sakamakon har zuwa Litinin bayan an bayyana na ƙananan hukumomi shida cikin takwas a ranar Lahadi.

Turawan zaɓe na wasu ƙananan hukumomi sun bayar da rahoton soke zaɓe a rumfunan zaɓe da dama saboda hatsaniya, da garkuwa da mutane, da sace malaman zaɓe.

Kazalika, da yawa daga cikin wakilan jam’iyyun da ke cibiyar tattara sakamakon sun yi watsi da sakamakon da aka gabatar tun ranar Lahadi, amma babban baturen zaɓe na jihar ya nemi su kai ƙorafinsu ga Inec a hukumance.

Zaɓen na Bayelsa ya fuskanci hatsaniya tun kafin fara kaɗa ƙuri’a, inda aka yi garkuwa da wata jami’ar hukumar zaɓe ta Inec kafin daga baya a sako ta.

Inec ta sake fitar da sanarwar cewa an yi garkuwa da wasu jami’an nata a ƙaramar hukumar Brass, waɗanda ba ta bayyana adadinsu ba.

Ƙuri’un da aka kaɗa

Masu katin zaɓe: 1,560,862

Masu zaɓen da aka tantance: 372,000

Jimillar ƙuri’un da aka kaɗa: 291,212

Ƙuri’un da aka soke: 3,658

www nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp