Gwamnan jihar Bauchi Sen. Bala Mohammed, ya bayar da umarnin rufe makaranta cikin gaggawa da wani matashi mai suna Mohammed Abidin Musa ya mutu.
An tsinci gawar Musa a cikin makarantar, tare da cire wasu muhimman sassan jikinsa da ake zargin masu tsafi ne.
Sai dai har yanzu ana kan zayyana cikakkun bayanai game da lamarin har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
Gwamnan ya bada umarnin ne a ranar Laraba a lokacin da ya kai ziyarar jaje ga iyalan mamacin a Gidan Bare-Bari.
Ya samu rakiyar kwamishinan ‘yan sandan jihar, Awal Musa Mohamed da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS.
Yayin da yake jajantawa ‘yan uwa, Mohammed ya yi kira ga iyaye da su rika lura da duk wani motsi na unguwanninsu.
Ya umurci hukumomin tsaro a jihar da su kara zage damtse wajen cafke wadanda suka aikata wannan aika aika.
Ya ce makarantar za ta ci gaba da kasancewa a rufe domin zurfafa bincike, inda ya ce gwamnatinsa za ta hada kai da jami’an tsaro domin ganin an gurfanar da masu laifin.


