fidelitybank

Gwamnan Bauchi dan Jagaliyar siyasa ne – Tinubu

Date:

Fadar shugaban kasa, ta yi kira ga gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya daina amfani da sukar gwamnatin Tinubu a matsayin hanyar wanke kansa.

A farkon makon nan ne wani bidiyon gwamnan ya ɓulla a shafukan sada zumunta, inda a ciki ya zargi gwamnatin Tinubu da bijiro da wasu manufofi da suka haifar da wahalhalu a ƙasar, musamman batun haraji.

A wata ziyara ta shugaban majalisar malamai ta ƙungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ga gwamnan na jihar Bauchi, Bala Mohammed ya buƙaci Shehin malamin ya faɗa wa Tinubu cewa manufofin gwamnatinsa ba sa aiki.

Cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare ya fitar, ya zargi gwamnan da gudanar da “siyasa irin ta jagaliya, maimakon mayar da hankali wajen magance matsalolin da jiharsa ke fuskanta”.

Ya ƙara da cewa “burin Shugaba Tinubu shi ne gina ƙasar ta hanyar haɗa kai da gwamnatocin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki.

”Shugaba Tinubu mutum ne mai sauraron jama’a, wanda ya aminta da gwamnatocin jihohi,” in ji shi.

Dangane da batun ƙudirin haraji kuwa, Sunday Dare ya ce shugaban ya bayyana ƙarara cewa duk wanda ke da magana kan ƙudirin to yana gaban majalisar dokokin ƙasar.

”Kuma yin fatali ko sukar wannan tsari ya saɓa wa dimokraɗɗiya”, in ji shi.

A saboda haka ne Sunday Dare ya buƙaci gwamnan na jihar Bauchi ya sauke nauyin da ke kansa na al’ummar jiharsa, maimakon tsayawa sukar gwamnatin Tinubu.

”Surutu da ihu da siyasar jagaliya ba za ta bari ya sauke nauyin mutanen Bauchi da ke wuyansa ba”.

Tun bayan ɓullo da batun harajin, gwamnan na Bauchi na daga cikin gwamnonin arewacin ƙasar da suka riƙa suka a kansa, saboda zargin zai cutar da yankin.

nigeria news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp