Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya musanta raɗe-raɗen da ake yi cewa yana shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar haɗaka ta ADC.
Wata sanarwa da gwamna Zulum ya fitar a shafinsa na X, ya ce wasu mutane ne kawai suka kirkiro da labarin don cimma wata manufa.
Zulum ya ce har yanzu yana nan daram cikin jam’iyyar APC.
“Mun samu labarin da ake yaɗa wa a kafafen sada zumunta cewa ina shirin komawa ADC tare da wasu gwamnoni biyar. Wannan labari ba shi da gaskiya, wasu ne kawai suka kirkiro shi domin janyo ruɗani.
“Har yanzu APC nake goya wa baya, da kuma ganin cigaban jihar Borno,” in ji Zulum.
Don haka gwamnan ya buƙaci al’ummar jihar da su yi watsi da labarin.
A ranar Laraba ne manyan ƴan adawar siyasa na Najeriya suka tabbatar da amincewa da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin wadda za su yi aiki da ita domin tunkarar zaɓen 2027.