Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a ranar Asabar ya sanar da bayar da kyautar Naira miliyan 100 kan wani Gift David Okpara Okpolowu, mai suna 2-Baba da wasu ’yan kungiyarsa, bisa wani mummunan kisan gilla da aka yi wa wani jami’in ‘yan sanda, Bako Angbashim.
An kashe DPO din ne a daren Juma’a a yayin da yake wani samame tare da mutanensa a cikin al’ummar Odiemudie, karamar hukumar Ahoada ta Gabas ta jihar.
Gwamna Fubara wanda ya bayyana kyautar a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, ya ce duk wanda ya bayar da bayanai masu amfani da za su kai ga kama wanda ake tuhuma tare da gurfanar da shi a gaban kuliya, za a ba shi ladan Naira miliyan 100.
A cewar gwamnan babban wanda ake zargi da kisan DPO ne ke da alhakin yin garkuwa da mutane da ta’addanci a wasu sassan jihar.
“Da farko dai, an bayyana wadanda ake zargin, Mista Gift David Okpara Okpolowu (aka 2-Baba) da dukkan mambobin kungiyarsa masu aikata laifin.
“Na biyu kuma, an ba shi kyautar naira miliyan dari (N100,000,000.00) ga duk wanda ya bayar da bayanai masu amfani da za su kai ga kama shi da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya.
Gwamnan ya kuma sanar da dakatar da wani sarki Eze Cassidy Ikegbidi har abada bisa zarginsa da hannu wajen kisan DPO.
“Na uku, Mai Martaba, Eze Cassidy Ikegbidi Eze Igbu Akoh II, an dakatar da shi har abada saboda laifin da ya yi na mikawa fitaccen David Gift da ‘yan kungiyarsa damar gudanar da ayyukansu cikin ‘yanci”, in ji shi.


