Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau.
Alhaji Abdulkadir zai ɗare karagar ne a matsayin Sarki na 16 na masarautar, inda zai maye gurbin mahaifinsa, Marigayi Mai martaba Dr. Ibrahim Bello, wanda ya rasu a ranar 25 ga watan Yulin 2025.
Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Suleman Ahmad Tudu ya fitar, inda ya ce an yi amfani da dokoki da tanade-tanaden doka ne wajen amincewa da naɗin wanda masu zaɓen sarkin masarautar suka zaɓa.
Sabon sarkin ne babban ɗan marigayin, kuma kafin naɗa shi sarki, shi ne Bunun Gusau.
Gwamna Lawal ya taya sabon sarkin murna, sannan ya yi kira gare shi da ya yi koyi da magabatansa, musamman ganin shi tsatson Malam Sambo Ɗan Ashafa ne.
Ya kuma yi kira ga sabon sarki ya dage wajen kira da samun haɗin kai da ci gaban masarautar Gusau da jihar, da ma ƙasar baki ɗaya.