An fashe da hawaye a wajen jana’izar wadanda harin ta’addancin da aka kai a cocin Saint Francis Catholic Church a garin Owaluwa a jihar Ondo a ranar 5 ga watan Yuni.
Gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu (SAN) ya kasa boye ra’ayinsa a yayin taron da aka gudanar a Mydas Resort and Hotel, Owo, a ranar Juma’a.
Akeredolu, wanda ya yi kuka a lokacin da yake jawabi, ya ce, gwamnati ta kasa kare wadanda harin ta’addancin ya rutsa da su.
Yayin da iyalan wadanda suka rasu da kuma masu juyayin suka yi ta zubar da hawaye, gwamnan ya ce gwamnati ta gaza wajen kare wadanda abin ya shafa da kuma daukacin al’ummar kasar.
A cewar Akeredolu, wanda ya yi ta kuka a duk lokacin da ya ke jawabinsa, ya ce, tsarin gine-ginen tsaron kasar na bukatar gyara. In ji Daily Trust.
Taron ya samu halartar uwargidan gwamnan, Betty, tsohon gwamna Mimiko da sauran manyan baki.
Akeredolu ya ce, “Abin da ya faru da mu a Owo, Jihar Ondo abu ne da ba za a iya misaltuwa ba. Har yanzu na yi imani cewa babu wata kalma da za ta kwatanta abin da ya faru. Muna da mutum 22 da suka rasu a wannan zauren yayin da aka binne wasu daga cikinsu.
“A kidaya na karshe, wadannan dabbobi sun kashe mutane 40. Mun kasa kare mutanen nan. Mun gaza ta fuskar tsaro. Waɗannan rundunan mugunta ba za su yi nasara a kanmu ba.