Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a ranar Juma’a ya bayar da umarnin a dawo da ‘yan majalisar dokokin jihar Kogi da aka dakatar.
Majalisar dai ta dakatar da mataimakin shugaban majalisar Ahmed Ahmed, shugaban masu rinjaye Abdullahi Bello da mataimakinsa Moses Ododo bisa laifin rashin da’a.
Amma Gwamna Bello, yayin da yake magana jim kadan bayan amincewa da kudurin kasafin kudin 2023, ya ce ya yafewa duk wanda ya yi masa laifi.
Ya kuma bukaci majalisar dokokin jihar da ta kira ‘yan majalisar da aka dakatar saboda ya jajirce wajen hada kan jama’a domin samun ci gaba a jihar Kogi.