fidelitybank

Gwagwarmayar sabon sakataren Gwamnatin Kano

Date:

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar.

Cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Sanusi Barure Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnan ya zaɓi Umar Ibrahim ne bisa ƙwarewar da yake da ita a fagen aikin gwamnati.

Gwamnan ya ce yana fatan sabon sakataren gwamnatin zai taimaka wajen inganta harkokin gwamnatin jihar.

“Muna sa ran zai taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da gwamnatin jihar gaba, don cimma manufofin da ta sa a gaba”, in ji sanarwar.

A watan Disambar shekarar da ta gabata ne Gwamna Abba ya sauke tsohon sakataren gwamnatin jihar, a wani garambawul da ya yi wa majalisar zartarwarsa.

Naɗin sabon sakataren zai soma aiki ne daga gobe Litinin 10 ga watan Fabrairu, a cewar sanarwar.

Wane ne sabon sakataren gwamnatin?

Umar Farouk Ibrahim ya samu digirinsa na farko a fannin kimiyyar siyasa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1985.

Ya fara aiki a shekarar 1987 zuwa 2023 lokacin da ya yi ritaya bayan shafe fiye da shekara 30 yana aiki, kuma ya riƙe manyan muƙamai ɓangarori daban-daban a fadin jihar, ciki har da babban sakataren dindindin a ofishin sakataren gwamnatin jihar daga 2001 zuwa 2015.

Haka kuma ya riƙe irin wannan muƙamin a ma’aikatar ayyukan gwamnatin jihar daga 2015 zuwa 2016.

Ya kuma riƙe muƙamin sakataren gwamnatin jihar na riƙo har sau biyu a 2013 da 2014 a lokacin da sakataren gwamnatin na wancan lokacin ya tafi hutu.

Ya kuma kasance cikin manyan kwamitocin gwamnati daban-daban.

today daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp