Ma’aikatar tsaron Rasha ta tabbatar da kama birnin Melitopol a ƙasar Ukraine.
Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya bayyana a matsayin gari mafi muhimmanci da aka ƙwace, tun lokacin da Rasha ta fara mamayar Ukraine a ranar Alhamis.
Melitopol na kusa da garin Mariupol, da ke yankin Kudancin Zaporizhzhya.
Ƴan Ukraine 150,000 ke zama a birnin Melitopol.