fidelitybank

Gurfanar da Hadi Sirika ya gamu da tutsu

Date:

Shirin gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Hadi Sirika da wani ɗan uwansa, Ahmad Sirika, a yau talata a wata sabuwar shari’ar kan badakalar kwangilar da ta kai naira biliyan 19.4 ya samu tsaiko sakamakon rashin kasancewarsu a gaban alƙali.

Gidan talbijin na Channels TV ya ce lauyan Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, Oluwaleke Atolagbe, ya shaida wa alkalin kotun, Mai shari’a Suleiman Belgore, cewa ba a sanar da tsohon ministan da dan uwansa abin da ake tuhumar su ba, a shari’ar.

Don haka lauyan ya buƙaci a ɗage shari’ar, buƙatar da alkalin ya amince da ita.

Daga baya alƙalin ya sanya ranar Alhamis 23 ga Mayu, 2024 a matsayin sabuwar ranar da za a gurfanar da su gaban kotu.

Hukumar EFCC na tuhumar tsohon Ministan ne da ɗan uwansa a wannan karon, da abubuwa takwas da suka jiɓanci tsabar kuɗi har naira biliyan 19.4.

Adadin dai an ce na wasu kwangilolin ma’aikatar sufurin jiragen sama ne daga tsohon ministan zuwa kamfanin Enginos Nigeria Limited wanda ake zargi mallakar ƙanin nasa ne.

A makon da ya gabata ne aka gurfanar da Sirika da diyarsa Fatima da kuma sirikinsa a gaban kotu kan zargin badaƙalar naira biliyan 2.7, inda daga bisani kotu ta bayar da belinsu.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp