Djurtus ta Guinea-Bissau za ta isa Abuja a ranar Talata 21 ga watan Maris, domin buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika na 2023 da Super Eagles ta kasa.
A ranar Juma’a 24 ga watan Maris ne za’a fafata a filin wasa na Moshood Abiola dake Abuja.
A cewar wani bayani a shafin intanet na hukumar kwallon kafa ta Guinea-Bissau, Djurtus za ta fara shirye-shiryen tunkarar wasan ranar Lahadi 19 ga watan Maris.
Karanta Wannan:Â Ina so Flying Eagles ta yaki duniya – Bosso
Daga nan ne ‘yan wasan da jami’ansu za su tafi Najeriya domin buga wasan bayan kwana biyu.
Za a sake fafatawar a Bissau a ranar Litinin, 27 ga Maris.
Super Eagles ce ke kan gaba a rukunin da maki shida a wasanni biyu, yayin da Guinea Bissau ke matsayi na biyu da maki hudu daga wasanni iri daya.