Sama da mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar Kogi 5000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).
‘Yan jam’iyyar APC sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP ne a ranar Lahadin da ta gabata a unguwar Avrugo da makwabciyarta a karamar hukumar Igalamela/Odolu a jihar Kogi.
Tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Igalamela/Odolu, Hon Collins’s Adama, wanda ya jagoranci sauran ‘ya’yan jam’iyyar zuwa PDP, ya ce APC ta gaza ‘yan Najeriya.
A cewar sa, lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su zabi rashin shugabanci na gari a zaben 2023, yana mai jaddada cewa duk wani kuskure da aka yi a yanzu zai haifar da da mai ido ga al’ummar kasar.
Adama, wanda shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Igalamela/Odolu, Honarabul Attai Ndamusa Salifu da dan takarar majalisar dokokin jihar Hon Umar Zakito suka tarbe su a cikin ‘ya’yan jam’iyyar PDP, ya kuma ce jam’iyyar APC mai mulki a shirye take ta kwashe kayanta daga jihar Kogi da kuma a matakin kasa.Ggu