fidelitybank

Guguwa ta kashe mutane uku a Taraba da Nassarawa

Date:

Rahotanni na cewa a kalla mutane uku ne suka rasa rayukansu a garin Takum da ke jihar Taraba sakamakon wata guguwa da ta faru sau biyu cikin kwana biyu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani mazaunin garin Mallam Maiwada Takum na cewa, guguwar ta soma faruwa ne da yammacin ranar Talata inda ta yi gagarumar ɓarna ga gidaje da makarantu da ofisoshi.

Takum ya ƙara da cewa da farko an yi mamakon ruwan sama daga bisani kuma aka yi guguwa mai ƙarfi da ta shafe fiye da sa’a ɗaya da rabi tana zagawa.

Shi ma wani mazaunin garin, Yakubu Adamu, ya bayyana cewa guguwar ta yi matuƙar ɓarna inda ta salwantar da gidaje da rayuka.

Babban mai bai wa gwamnan jihar shawara kan yaɗa labarai, Emmanuel Bello ya ce gwamna Agbu Kefas ya higa garin domin duba irin ɓarnar da guguwar ta yi.

An kuma bayar da rahoton mutuwar mutum ɗaya da jikkatar wasu da dama sakamakon tashin guguwa da ta lalata gidaje fiye da 100 a yankin Agbashi da ke ƙaramar hukumar Doma a jihar Nassarawa.

Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, John Bako-Ari ne ya tabbatar da lamarin inda ya ce guguwar ta tashi ne ranar Talata da yamma.

breaking news in nigeria today punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp