Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar Mali, ba tare da an cimma wata yarjejeniya kan lokacin da za a yi zaben da zai mayar da kasar tafarkin Dimukradiyya.
Gwamnatin Mali da ta karbe ikon kasar shekarar 2020, ta ce, ba ta ji dadin yadda aka kasa cimma matsaya ko tartibiyar magana ba.
Mr Jonathan dai shi ke shiga tsakani a madadin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO,ya kuma je ne da niyyar tsaida lokacin da za a yi zabe, sakamakon korafin shekaru biyar sun yi yawa karkashin mulkin soji.
Kungiyar ECOWAS da Tarayyar Turai sun kakabawa mambobin gwamnatin rikon Mali takunkumi, ciki har da ‘yan gaban goshin shugaba Assimi Goita.