fidelitybank

Gombe: ‘Yar Majalisar dokoki ta sauya sheka daga PDP zuwa APC

Date:

Mace daya tilo a majalisar dokokin jihar Gombe, Honourable Asma’u Mohammed Iganus ta jam’iyyar PDP ta jagoranci magoya bayanta wajen ficewa daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC.

Da ya ke karbar Asma’u Iganus mai wakiltar mazabar Jihar Shongon da Magoya bayanta na jam’iyyar PDP a APC, Gwamna Inuwa ya tabbatar wa ‘yar majalisar a shirye ya ke ya yi mata aiki, domin ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a 2023 da ma gaba.

An gudanar da liyafar karbar ‘yar majalisar ne a Lapan, karamar hukumar Shongom inda Gwamna Inuwa shi ma ya nuna jin dadinsa da karbar ta da magoya bayanta.

Ya yaba da hazakar siyasar Hon. Asma’u Iganus ta ce ta koma jam’iyyar APC ba bisa katsa landan ba, amma zabin da na yi ya yi nuni da irin rawar da jam’iyyar ke takawa a jihar.

Gwamnan ya ce, “Tun kafin ta yanke shawarar komawa jam’iyyar APC, ta taba zuwa wurina ta gabatar da koke a kan bukatar sake gina gada a mazabarta kuma na biya mata bukatunta, kuma na yi aikin ba tare da wata tangarda ba”.

A cewar Gwamnan, gwamnatin APC a jihar Gombe ta himmatu wajen aiwatar da manufofi da shirye-shirye masu tasiri kai tsaye ga rayuwar al’ummar jihar.

Ya ce,”Shigowar Asma’u da magoya bayanta sama da 2000 ba zai iya zuwa ba a daidai lokacin da gwamnatin APC a jihar ke samar da yanayi mai dorewa na zamantakewa da tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa da za su kasance a cikin al’umma, dadewa ya samar da ayyukan yi ga dimbin matasan jihar”.

Ya bayyana cewa aiwatar da shirin gina titin ‘Network 11-100’ ya na ci gaba da tafiya kamar yadda a ka bayyana a cikin takardar manufofin gwamnatinsa tare da tabbatar wa al’ummar Karamar Hukumar Shongom cewa nan ba da jimawa ba za a fara hanyoyin da su ka hada Filiya zuwa Gundali da Lapan zuwa Burak.

sun news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp