Kungiyar kwallon kafa ta Gombe United ta kara wa ‘yan wasanta karin sabbin ‘yan wasa biyar gaba da wasannin zagaye na biyu a kakar wasa ta bana.
A cikin jerin sunayen akwai dan wasan tsakiya Mathias Samuel, wanda ya zo daga Lobi Stars Football Club na Makurdi.
Dozie Umeh ya koma ne daga wata kungiyar kwararrun kwallon kafa ta Najeriya, Abia Warriors.
Karanta Wannan: Super Eagles za ta farfado a wasan gaba da Guinea-Bisau – Iwobi
Winger Paul Obata da dan wasan gaba Igbudu Igbada sun koma kungiyar daga El Kanemi Warriors na Maiduguri, yayin da Wasiu Mamud, dan wasan gefe ya koma kungiyar daga Kwara United.
Savannah Scorpions za su kasance baƙi na Plateau United a sabon filin wasa na Jos ranar Lahadi.