Mai alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar Muhammad Sa’ad Abubakar, ya tabbatar da cewa, gobe Asabar za a tashi da Azumin watan Ramadan a Najeriya.
Sarkin Musulmin ya tabbatar da hakan ne a lokacin da ya samu rahotonnin ganin sabon jinjirin watan Ramadana a Najeriya.
An dai ga watan ne a Zazzau, Zamfara, Abuja, Legas da dai sauransu.
Gobe Asabar zai kasance 1 ga watan Ramadan shekarar har hijar 1443.