Kotun daukaka kara ta sanya Juma’a, 17 ga watan Nuwamba, a matsayin ranar yanke hukunci kan karar da gwamnan Kano ya daukaka, inda yake kalubalantar soke nasarar zabensa.
Abba Kabir Yusuf ya garzaya gaban kotun daukaka kara, bayan kotun korafin zabe ta jihar Kano a ranar 20 ga watan Satumba, ta rushe nasarar da ya samu, inda ta ce abokin takararsa na jam’iyyar APC Nasir Yusuf Gawuna ne halastaccen wanda ya ci zabe.
Kotun dai ta kafa hujjar hukuncin da ta yanke ne a kan kuri’u sama da 165,000 da ta soke daga cikin abin da Abba Kabir Yusuf na NNPP ya samu, saboda rashin sa hannu da kwanan wata da kuma hatimin hukumar zabe. Jam’iyyar APC, ita kuwa ta roki kotun ta yi watsi da karar da Gwamna Abba Kabir ya daukaka.
Hukuncin kotun daukaka karar na zuwa ne kwana goma cif bayan alkalan kotun da ke zama a Abuja, sun saurari bahasin dukkan bangarorin da ke cikin shari’ar, tare da sanya hukuncinsu a mala, sannan suka ce za su sanar da ranar yanke hukunci nan gaba.
Wata takardar kotun daukaka kara da BBC ta gani, ta lissafa APC da NNPP da kuma INEC a matsayin wadanda ake kara. Sannan ta ce kotun za ta fara zaman yanke hukunci daga misalin karfe 9:00 na safe.
Shari’ar zaben gwamnan Kano na daya daga cikin shari’o’in zabe mafi muhimmanci tun bayan kada kuri’a a babban zaben kasar cikin watan Fabrairu da Maris.
Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya tana fatan kotu za ta dawo mata da kujerar gwamna, wadda ta kubuce daga hannunta, zuwa hannun jam’iyyar adawa ta NNPP, yayin da NNPP ke alla-alla ta tsira da kujerar gwamna daya tilo da ta samu bayan zaben 2023.