Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta tsayar da ranar Laraba 20 ga watan Satumba, 2023, domin yanke hukunci kan karar da jam’iyyar APC ta shigar kan Gwamna Abba Yusuf na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP.
Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, shugaban kwamitin mutane uku, ya ce za a yanke hukuncin ne kafin kwanaki 180 da doka ta ba su.
Dage zaman ya biyo bayan jawaban karshe da bangarorin biyu suka yi.
Yayin da ta ke gabatar da jawabi na karshe ga kotun, APC ta bukaci kotun da ta tabbatar da karar da ta shigar ta kuma mayar da Nasir Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.
INEC, NNPP da Yusuf sun bukaci kotun da ta yi watsi da karar.


