Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC ta tabbatar da mutuwar mutan biyu, bayan da wata motar dakon mai ta kama da wutaa hanyar Legas zuwa Ibadan.
Kwamandan sashen hukumar, Ahmed Umar ne ya shaidawa manema labarai cewa, hatsarin ya auku ne da misalin karfe 6.05 na safe kusa da kamfanin CDK.
Ya bayyana cewa, motar dakon mai, wacce ba ta da lambar rjjista, ta na kan hanyar Legas zuwa Ibadan a lokacin da ta fashe a wasu ’yan kilomita a yankin Sagamu.
Ya kara da cewa, lamarin ya rutsa da maza takwas da motoci uku da kuma babur kirar Bajaj.
Umar ya kuma ce,“Mutane biyu ne suka mutu, yayin da a ka ceto mutane shida ba tare da sun jikkata ba”.