A Birtaniya, yanayin zafi ya kai maki arba’in a ma’aunin Celsius a karon farko, yayin da tsananin zafin ke ci gaba da ratsa ƙasashen yammacin Turai.
Ofishin kula da yanayi na ƙasar ya ce an samar da irin waɗannan alkaluman fiye da sau goma daga sauyin yanayin da dan Adam ke haifarwa.
Belgium da Netherlands da Jamus su ma suna fuskantar ƙaruwar matsanancin zafin. In ji BBC.
Amma zafin ya ragu a kudu maso yammacin Turai, ko da yake har yanzu wutar daji na ci gaba da barazana a sassan Faransa da Sifaniya