fidelitybank

Gobarar California ta laƙume rayukan Mutane 10

Date:

Jami’ai a birnin Los Angeles sun ce mummunar gobarar daji ta lalata sama da gidaje dubu 10 da wasu gine-gine a jihar Californian Amurka.

Kawo yanzu adadin waɗanda aka tabbatar da mutuwarsu ya kai 7, ana kuma ci gaba da neman wasu.

Brad Sherman ɗan majalisa ne mai wakiltar Carlifornia, ya bayyana halin da ake ciki, inda ya ce wannan ce gobara mafi muni a tarihin Amurka.

Ya ce babu wanda ya taɓa tsammanin lamarin zai kai haka ga kuma iska mai ƙarfin da ake fama da ita na ƙara rura wutar.

Ƙiyasin ɓarnar da wutar dajin ta yi ya tashi sosai zuwa aƙalla dala miliyan 135.

An tura jami’an tsaro na ƙasa 400 a yankin domin taimaka wa ƴansanda aikin, bayan da aka samu rahotanni sata ko kwashe kayan jama’a. In ji BBC.

Da yake magana a wani taron manema labarai , babban jami’in ƴansanda na birnin na Los Angeles, Jim McDonnell, ya ce abin da suka mayar da hankali yanzu a kansa shi ne kare aikata miyagun laifuka.

Ya ce, “kare gidaje da harkokin kasuwanci a wuraren da aka kwashe jama’a da inda babu tsaro sosai shi ne abin da muka bayar da fifiko a kai yanzu, domin tabbatar da ganin cewa babu wanda ya yi amfani da damar mawuyacin halin da ake ciki. Ko kaɗan ba za a lamunta wawashe kayan jama’a ba ko wawason kaya ko ribatar wannan bala’i.”

benue news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...
X whatsapp