Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, ta tabbatar da aukuwar gobara a ofishinta da ke jihar Enugu.
Gobarar ta cinye ɗaya daga cikin gine-ginen da ke cikin Rundunar Yanki.
Shugaban yada labarai na EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar da wata sanarwa da yammacin jiya Juma’a.
“Lamarin da ya faru da misalin karfe 12:30 na safiyar Juma’a, ya samo asali ne sakamakon karuwar wutar lantarkin da jama’a ke yi.
“Daga baya an kashe gobarar ta hanyar hadin gwiwar hukumar kashe gobara ta jihar Enugu da ta tarayya,” inji shi.
Kakakin ya kara da cewa ba a samu asarar rai ba a lamarin.