Aƙalla ɗaliban uku ne suka jikkata bayan wata sabuwar gobara ta tashi a wata makarantar kwana ta mata da ke tsakiyar ƙasar Kenya.
‘Yansanda sun ce gobarar ta lalata ɗakunan kwanan ɗalibai. Kawo yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba.
Lamarin na zuwa ne ƙasa da kwana uku da wasu ɗalibai 21 suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a makarantar kwanan ɗalibai ta maza a gundumar Nyeri da ke gabashin birnin Nairobi.
Gobara a makarantun kwana a Kenya na neman zama ruwan dare, inda a lokuta da dama hukumomi ke ɗora alhakin hakan kan bata gari.