Kimanin shaguna 150 ne a kasuwar ‘Yan Katako da ke Sabon Gari, Zariya a Jihar Kaduna gobara ta kone su kurmus.
Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1 na safiyar ranar Laraba, inda ta ci gaba da ci har zuwa la’asar.
Babban jami’in tsaro na kasuwar, Hamisu Buhari ya bayyana cewa, gobarar ta fara ne a lokacin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kaduna ta kawo wutan lantarki, inda wata igiyar wutar lantarki ta fado a rufin daya daga cikin shagunan.
Ya kuma bayyana cewa, kokarin jawo hankalin hukumomin kashe gobara a yankin ya ci tura.
Ya bayyana cewa, shi da kansa ya je ofishin hukumar kashe gobara ta Kofar Doka, amma an sanar da shi cewa motar da suke aiki ba ta da kyau.
Ya ce, “A karshe na tuntubi hukumar kashe gobara a babbar kasuwar Sabon Gari. Sun ce in ba su man fetur, wanda na yi kafin su zo wurin.”
Alhaji Alin Ashiru, shugaban dillalan katako a kasuwar ya alakanta gobarar da tartsatsin wutar lantarki.
Ya kuma kara da cewa, kimanin shaguna 150 ne suka kone kurmus, tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin naira.
Abdul Azeez Abdullahi shugaban hukumar KEDCO ya musanta cewa, wutar lantarki ce ta haddasa gobarar.
Ya yi zargin cewa, rahotannin da aka samu sun nuna cewa, gobarar ta tashi ne a daya daga cikin shagunan kasuwar ta kuma bazu zuwa wasu shaguna.