Wata gobara ta lalata dukiya ta miliyoyin naira a Ilorin, babban birnin jihar Kwara a ranar Juma’a.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 09.52 a lamba 138D, unguwar Temidire Irewolede, a karamar hukumar Ilorin ta yamma.
Daga cikin gidaje hudu da ke ginin daki daya ne abin ya shafa, kamar yadda kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Hassan Adekunle, ya bayyana a wata sanarwa a Ilorin.
Ya kara da cewa babu wani rahoto da aka samu na asarar rayuka, yayin da ake alakanta musabbabin tashin gobarar da wutar lantarki.
Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Prince Fala.


