Wata gobara ta tashi a wani gidan rediyo mai zaman kansa, Kpakpando FM, Mbaukwu a karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra.
Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 9:30 na yammacin ranar Alhamis, ya lalata ginin ofishin, tare da kona wani bangare na kayan aikin studio din.
Shugaban hukumar kashe gobara na jihar, Engr Martin Agbili, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ba a yi asarar rai ba, an kuma ceto wasu kayan aiki ta hanyar mayar da martani ga mutanensa.
“Da misalin karfe 2139hrrs (9.39pm) na ranar Alhamis 07-03-2024, hukumar kashe gobara ta jihar Anambra, ta samu kiran tashin gobara a gidan rediyon KPAKPANDO FM, MBAUKWU.
“Nan da nan muka tura motar kashe gobara da jami’an kashe gobara zuwa inda gobarar ta tashi. Mun yi yaƙi, mun sarrafa kuma muka kashe wutar.
“Ba a san musabbabin tashin gobarar ba. Ginin ofishin da na’urorinsa na studio ya kone wani bangare yayin da aka ceto wasu kayan aiki da sauran sassan ginin.
“Mun janye daga wurin da gobarar ta tashi da misalin karfe 2318 na safe 11:18 na dare”, in ji shi.