Wata gobara da ta tashi a ranar Juma’a a ma’ajin wajen hukumar agajin gaggawa ta jihar Kano (SEMA) ta lalata wasu kayayyaki masu daraja da kudinsu ya kai Naira miliyan 18.5 a Mariri dake karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.
Sakataren zartarwa na SEMA, Saleh Jili, ya tabbatar da tashin wutar yayin da yake yiwa manema labarai jawabi.
Ya ce, kayayyakin agajin ke ciki na bayar da tallafin gobara da ambaliyar ruwa ne da ake bayar wa wanda ta shafa.
Ya bayyana cewa, kayayyakin da da wutar ta lalata sun hada da katifu guda 450, matashin kai 450, katan 655 na pampers na manya da yara.
Sauran kayayyakin da kudinsu ya kai Naira 18.5m da suka kone sun hada da katon na Dettol guda 10, kwali 10 na sinadarin wanke-wanke, kwali 10 na Izal, injin nika, injin dinki, injinan Vulcanizing na faci da gidan sauro da dai sauransu.
“Jami’an mu za su tantance irin barnar da aka yi da kuma kudin da za a biya, domin mika wuya ga gwamnati domin taimako.”
Ya bukaci jama’a da hukumomin makaranta da su yi hattara da kona daji.