fidelitybank

Gobara ta kona shaguna 37 a Kano

Date:

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce, gobara ta kone shaguna 37 a unguwar Zawaciki da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN cewa gobarar ta faru ne da misalin karfe 01:37 na safiyar Laraba.

A cewar Abdullahi, da misalin karfe 01:37 na safe ne muka samu kiran wani Malam Baba cewa an samu tashin gobara a Zuwaciki.

“Mun yi gaggawar tattara jami’an mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 01:47 na safe, muka kashe gobarar domin kada ta bazu zuwa wasu shaguna,” inji shi.

Abdullahi ya ce shagunan 37 sun kasance a kasan bene na wani gini mai amfani da yawa.

Ya kuma kara da cewa gobarar ta dan yi barna a wasu shaguna uku.

A cewarsa, ba a samu asarar rai ba, kuma ana kan binciken musabbabin tashin gobarar.

bbc news nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp