Gobara ta kone wasu sassan kasuwar karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa, inda ta lalata rumfuna da dukiyoyi masu daraja.
Kakakin hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC, Adamu Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 4 ga watan Disamba 2022 da misalin karfe 11:15 na safe a kasuwar Kiyawa.
Adamu ya bayyana cewa gobarar da ta tashi da misalin karfe 10:30 ta lalata rumfunan kasuwa sama da 20 da wasu kayayyaki masu daraja ta miliyoyi.
Ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, in ji hukumar NSCDC.
Shaidun gani da ido sun ce gobarar na iya rasa nasaba da wani wurin juji da ke kusa da kasuwar da aka kona don kone tarkace.