Wani jariri dan watanni biyu, mace mai juna biyu, da wasu mutane biyu sun mutu a wani hatsarin gobara da ya afku a Bonny/Nembe/Bille Jetty da ke Fatakwal a jihar Rivers da safiyar ranar Litinin.
POLITICS NIGERIA ta samu labarin cewa, jiragen ruwa kusan 60 ne suka kone a gobarar.
Wutar ta tashi ne da misalin karfe biyu na safe. Duk da cewa ba a san musabbabin tashin gobarar wanda shi ne karo na biyu cikin kasa da wata hudu ba, amma wasu mazauna yankin sun ce, watakila ba a rasa nasaba da ma’ajiyar man fetur da aka tace ba bisa ka’ida ba a jirgin, wanda aka fi sani da kpofire a cikin jirgin.
Gobara ta karshe da ta barke a jirgin dai ta faru ne a watan Nuwambar shekarar 2021. Mutane da dama ne suka kone tare da kona dukiyoyin da aka kiyasta kimanin miliyoyin Naira.
Jetty galibi wurin jigilar jama’a ne ga dubban mazauna da ke tafiya daga Fatakwal ta teku zuwa Bonny, Bille, Nembe, da sauran al’ummomin kogi.