fidelitybank

Gobara ta karu a Kano saboda shigowar hunturu – ‘Yan Kwana-Kwana

Date:

Hukumar kashe gobara a Kano ta ce an samu ƙarin tashin gobara a faɗin jihar sakamakon shigowar yanayin hunturu.

Kakakin hukumar Saminu Yusuf Abdullahi ya ce, kafin zuwan yanayin hunturun an samu raguwar tashin gobara a jihar – wadda ita ce cibiyar kasuwancin arewacin ƙasar.

Saminu Yusuf Abdullahi ya ce a watan Nuwamban da ya gabata kaɗai an samu tashin gobara a jihar har sau 43, sakamakon yadda mutane ke ƙara ta’ammali da wuta a lokacin na hunturu.

”Adadin ya ninka, domin a watan Oktaba an samu matsalar tashin gobara a Kano sau 24, amma sakamakon shigowar hunturu a watan Nuwamban adadin ya kai 43”, in ji shi

Ya kuma ce daga shigowar watan Disamba, zuwa yanzu hukumarsu ta samu labarin tashin gobara har sau bakwai, zuwa yanzu.

Haka kuma hukumar kashe gobarar jihar ta ce mutum uku sun mutu, yayin da aka yi asarar dukiya da ta kai naira miliyan 130, a cikin watan da ya gabatan sakamakon tashin gobarar.

legit ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp