Wata gobara da ta tashi a birnin Kano ta yi sanadiyyar ƙona mota ɗaya tare da ƙone ramukan saukewa da haɗa Ƙwalta.
Wutar ta fara ci ne da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar yau Laraba a kan Titin Hadeja.
Wakilin BBC a Kano ya ce har zuwa ƙarfe 9:50 ba a kashe wutar ba.
Sai dai kawo yanzu ba a san musababin tashin gobarar ba, tare da sanin irin asarar da ta yi a wajen.