An samu tashin gobara da sanyin safiya a hukumar jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) da ke Yaba, ofishin kasa da ke Legas.
Wani rahoto da aka sanyawa hannu a gidan rediyon Legas Bond FM, ya nuna cewa jami’an kashe gobara daga Jami’ar Legas (UNILAG) da Kwalejin Fasaha ta Yaba (YABATECH) sun isa wurin da lamarin ya faru domin kashe gobarar har zuwa lokacin gabatar da rahoton.
Wani ganau ya ce an ga wasu ma’aikatan Majalisar da ake kyautata zaton sun makale ne a tsakanin wasu benaye suna yunkurin tsallakewa ta tagar babban bene mai hawa 12 domin tserewa shakewa.
Har yanzu kawo wannan lokacin babu wani karin bayani daga bakin mahukuntan.