Wata gobara da ta tashi ranar Talata a Kano ta ƙone tankokin dakon mai biyar waɗanda ke ɗauke da mai, mai yawan lita 20,400.
Bayanai daga hukumar kashe gobara ta jihar Kano, sun ce lamarin ya faru ne a wani gini da ake amfani da shi a matsayin rumbun adana mai a Farawa Kwanar Yashi da ke babban birnin jihar.
Mai magana da yawun hukumar ya ce ba a samu rasa rai ba a lokacin gobarar, sai dai wasu mutum uku na samun kulawa a asibiti.
Bayanan sun nuna cewa, gobarar ta tashi ne daga wani ƙaramin janareto da ake amfani da shi wurin samar da wutar lantarki a ginin. In ji BCC.