An samu tashin gobara da safiyar yau Alhamis, a kasuwar kayayyakin ƙarafuna ta Olowu da ke jihar Legas.
Wasu shagunan da gobarar ta cinye na dauke da na’urorin sanyaya na’urorin sanyaya iska, da sassan ababan hawa, da babura da dai sauransu.
‘Yan kasuwar sun kirga asarar da suka yi domin kayayyakin da gobarar ta ƙona sun kai na miliyoyin naira.
Mutanen hukumar kashe gobara ta jihar Legas da jami’an tsaro suna wurin. An shawo kan lamarin.
Irin wannan lamari ya faru makonni uku bayan da kasuwar Akere Spare Parts da ke kan titin Kirikiri, Olodi-Apapa a Ajegunle, ta kama da wuta.