Gobarar daji na ci gaba da ruruwa a sassan wasu ƙasashen Turai, ciki har da tsibirin Iberia da Girka da kuma ƙasashen yankin Baltic.
Yanzu haka ana fama ana ci gaba da fama da tsananin zafi a yankunan.A Sifaniya, akwai gomman wurare da wutar ke ci.
An kwashe fiye da mutum 4,000 daga lardin León da ke arewa maso yammaci a jiya da dare. Wani ma’aikacin kashe gobara na sa-kai ya mutu a yankin.
Wani mazaunin ƙauyen Piperi ya bayyana yadda lamarin ya fa faru, yana mai cewa lammura sun hargitse a jiya inda iska ta zo da ƙarfi wadda ta sa wutar ta yaɗu cikin sauri.