‘Yan Democrats a Amurka sun zargi Donald Trump da mutumin da giyar mulki ke ruɗawa, bayan ya ce zai tura jami’an rundunar tsaro ta ƙasar birnin Washington don yaƙi da laifukan da ake ganin sun gagari ƴansandan birnin.
Magajiyar birnin Muriel Bowser, ta ce matakin bai dace ba, sannan ta musanta batun da shugaban ke yi cewa an gaggara daƙile masu aikata laifi.
‘Yan Democrats a majalisa, sun ce wannan mataki babu wani abin da zai haifar face ‘tsoro da hargitsi, kuma wannan yunƙuri ne kama hanyar kama-karya.
Shugaban masu rinjaye a majilsar wakilai ya ce Mista Trump ya mayar da mulki kamar wata sarauta.
Shi dai Trump ɗin ya ce birnin washington a cike yake da masu gararamba a tittuna suna aikata miyagun ayyuka kuma dole ya kawo gyara.