fidelitybank

Girgizar kasar Myanmar ta kashe Masallata 170

Date:

A yayin da aka yi kiran sallah a birnin Sagaing a ranar Juma’ar da ta gabata, ɗaruruwan Musulmai ne suka gaggauta zuwa masallatai biyar da ke birnin da ke tsakiyar Myanmar.

Sun tafi domin yin sallar Juma’ar ƙarshe a watan Ramalana, ƴan kwanaki gabannin bikin sallar idi.

Sai dai ƙarfe 12:51 agogon ƙasar, sai aka samu girgizar ƙasa. masallatai uku suka rushe, cikinsu har da mafi girma na Myoma, kuma kusan dukanin mutanen da ke ciki suka mutu.

Can wasu ɗaruruwan kilomita a masallacin Soe Nay Oo da ke garin da ke bakin iyakar Thailand na Mae Sot, shi ma girgizar ƙasar ta shafe shi.

Kwana ɗaya bayan girgizar ƙasar ne tsohon limamin masallacin Myoma ya gano cewa kimanin mutane 170 ciki har da ƴan uwansa da abokai da masu binsa sallah a baya, duka sun mutu a cikin masallacin.

Wasu daga cikinsu ƙusoshi ne a ƙungiyar al’ummar musulmi.

Fiye da mutane 2,700 ne suka mutu a girgizar ƙasar da ta auku a kusa da Sagaing da Mandalay, birni na biyu mafi girma a Myanmar.

Adadin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasar na ƙaruwa, yayin da ake ci gaba da tono gawawwaki daga ƙarƙashin baraguzai.

tribune news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp