Jiragen Saudiyya shida ɗauke da kayan agaji sun isa Turkiyya, dpomin tallafa wa waɗanda iftila’in girgizar ƙasa ya shafa.
Kayan agajin mai nauyin tan 98 ya ƙunshi kayan abinci da tantuna da barguna da kuma magunguna.
Sarkin Saudiyya Salman bin Abdula’ziz tare da yarima mai jiran gadon sarauta Mohammed Bin Salman suka bayr da umarni kai kayan tallafin.
Ana sa ran rarraba kayan tallafin uwa wuraren da girgizar ƙasar ta shafa a ƙasashen Turkiyya da Siriya. In ji BBC.