Gwamnatin Indonesiya ta yi alƙawarin taimakawa da kudaden sake gina gidaje kusan dubu 20,000 wadanda girgizar kasa ta lalata a yammacin Java ranar Litinin.
Da yawa daga cikin mutanen da suka tsira suna kwana ne a tantuna saboda tsoron komawa da suke yi muhallansu kasancewar har yanzu kasar na kara gyara zama.
Mutum 268 aka tabbatar sun rasu amma kuma hukumomi sun ce, har yanzu akwai wasu akalla 150 da ba a san inda suke ba.
Masu aikin ceto sun shafe dare na biyu suna nema cikin ɓaraguzai.
Waɗanda suka ɓata sun haɗa da yara da yawa wadanda gini ya rufe makarantarsu lokacin da kasar ta girgiza.