fidelitybank

Girgizar Kasa: An tsinci gawar ɗan wasan Ghana Atsu a Turkiyya

Date:

An tsinci gawar ɗan wasan Ghana Christian Atsu, a ƙarƙashin ɓaraguzan gidansa, kamar yadda wakilin ɗan wasan ya bayyana, kusan makonni biyu bayan da girgizar ƙasa ta afka wa Turkiyya da Siriya.

Atsu mai shekarar 31 ya yi wasanni a ƙungiyoyin Chelsea da Newcastle.

Tun bayan girgizar ƙasar – da ta lalata gidaje da dama a birnin Hayat inda ɗan wasan ke zaune – ba a sake jin ɗuriyar ɗan wasan ba.

Tun da farko ƙungiyarsa ta bayyana cewa an kuɓutar da shi da munanan raunuka, to sai dai daga baya, wakilinsa ya tabbatar da cewa ba a ceto shi ba.

“Cikin mummunan tashin hankali da firgice, nake sanar da masu yi wa Atsu fatan alkairi cewa an gano gawarsa da safiyar yau,” kamar yadda wakilinsa Nana Sechere ya bayyana a shafinsa na Tuwita.

“Ina miƙa sakon ta’aziyyata ga iyalai da masoyansa. ina kuma so na yi amfani da wannan dama wajen mika godiya ga duka mutane game da addu’o’i da goyon bayan da suke ba shi”.

sspdf news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp