fidelitybank

Gini ya turmushe mutane uku a Rivers

Date:

Mutum uku sun mutu bayan da wani gini da ba a ƙarasa ba ya faɗi a garin Ngbodo a ƙaramar hukumar Ikwerre na jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Rahotonni sun ce faduwar ginin mai hawa biyu ya yi sanadin mutuwar leburori uku da ke aikin ginin.

Karanta Wannan: An ceto mutane 24 da ginin Abuja ya danne su

Babban kwamandan hukumar tsaro ta Civil Defense na jihar Michael Ogar wanda ya jagoranci jami’an hukumar wajen aikin ceto leburorin, ya danganta lamarin da rashin amfani da ingantattun kayan aikin gini.

A wata sanarwar da hukumarsa ta fitar ta ce binciken farko ya nuna cewa rodi da filoli da bulon da aka yi amfani da su wajen ginin ba su da ingancin da ake buƙata.

Faɗuwar gine-gine musamman waɗanda ba a kammala ba, ba sabon abu ba ne a kasar nan, domin kuwa ko a cikin makon da ya gabata ma wani ginin da ba a kammala ba ya fadi a Abuja babban birnin ƙasar.

kano news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp