Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar mutane biyu sakamakon ruftawar wani gini da ya afku a karamar hukumar Nomansland Faage dake jihar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Saminu Yusuf Abdullahi ya ce kawo yanzu an ceto mutane biyu da ransu aka kai su asibiti, yayin da biyu kuma suka mutu yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
Ya bayyana cewa lamarin da ya kai ga rugujewar ginin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 2 na safe yayin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya.
An ce ginin ya ruguje ne sakamakon ambaliya da ruwan ya yi wanda ya shafi ginin da ke kusa da mashigar ruwa.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano ta bayyana a ranar Laraba cewa mutane 31 ne suka mutu sannan kuma gidaje 5,280 suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa a jihar.