Wani gini mai bene uku ya rufta a unguwar Legas Island a safiyar Alhamis, lamarin da ya jikkata wasu daga cikin mazauna gidan.
Ginin da ke kan titin Asesi, kusa da titin Adeniji Adele, ya rufta ne kwatsam ba tare da sanin abun da ya haddasa hakan ba.
Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Gbenga Omotoso ne ya tabbatar da ruftowar ginin a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya ce “An ceto mutane hudu daga cikin baraguzan ginin kuma an garzaya da su asibiti,” in ji Kwamishinan.
Jami’an ceto daga hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) da sauran hukumomi sun isa wurin da lamarin ya faru domin gudanar da ayyukan ceto.